Tuesday, 4 February 2020

BLOGGING: YADDA AKE BUDE BLOGGER WEBSITE

[04/02, 10:58 a.m.] Khaleed_Teejohn: *BLOGGER CLASS*

*Yadda zaku samu kudi ta hanyar mallakar website*

Assalamu alaikum yan,uwan, kamar de yanda na alkawarta muku kan cewa a yau zan fara koyar da darasi akan blogger wato yanda zaku samu kudi a online ta hanyar mallakar website

Kamar yadda a baya muja koyar da youtube tun daga farko har karshe, wanda shima kaface da ake samun makudan kudade, to ganin hakane yasa nace yakamata na kawo hanyar samun kudi ta blog domin wadanda suka gagara youtube saiku koma blog kokuma in mutum yana ta lokaci yayi dukka biyun

to amma agaskiyar magana blog yafi youtube sauki, domin kuwa shi basa bukatar wani adadi na mabiya kokuma makallah wato masu kallo, su kawai abun da suke bukata shine ka tsara site dinka yayi kyau sannan kuma kana kawo lbr ko wani abun da kakeyi masu ma,ana, sai kuma ka sayi domain wanda shima baya wacu 1k to 3k zamuyi bayaninsa anan gaba, to idan ka cika wadannan ka,ida insha Allah saide kaji kudi suna sauka acc dinka, domin kuwa suma ana samun kudade masu matukar yauwa, karamin albashi a wata shine $100 wanda yake dede da 36'000 to kunga ko iya 36k kake samu duk wata ai zaka rage zafi, ballema saika samu ninkinsa sau uku, a wata, ya danganta da yanda ka dage da aikinka, domin idan suka karbeka to masu zuwa blog dinka suna karanta abun da kakeyi to ta hakane zasuna biyanka, sannan kuma ku sani tafiyar da blog bazai hanaka aiwatar da Al,amurankaba domin kuwa shi yana da sauki ba kamar youtube ba, sabi da haka ga bayin blog nan ku karanta shi akasa domin ku sake fahinta
👇🏻👇🏻
[04/02, 10:58 a.m.] Khaleed_Teejohn: 3. Shin Blogging Yana Bukatar Kashe Kudi?
Akwai Blogging na kyauta akwai kuma wanda sai mutum ya
kasha kudi, sai dai wanda ya kashe kudi shine zai fi cin ribar
dake cikin blogging.
Sannan akwai abubuwan da wanda ya biya kudi zai iya yi
amman wanda bai biya ba ba zai iya yi ba.
Sannan misali wanda ya biya kuna samun mutane adadi
daya to kudin da wanda ya biya zai samu to kai zaka samu
rabinsa ne.
[04/02, 10:58 a.m.] Khaleed_Teejohn: 1. Menene Blog?
Blog daya ne daga cikin shafukan internet da ake sanya
bayanai a yanar gizo, ta yadda idan ka shiga zaka ga
bayanan da aka sanya akansa.
Dai-daikun mutane da kungiyoyi kan mallaki blog domin
adana bayanansu a yanar gizo.
2. Yaushe Aka Fara Yin Blog A Duniya:
A karni na 9 aka fara harkar blogging a duniya inda mutane
kan wallafa bayanan da ya shafi rayuwarsu akai, sai dai ana
yinsa ne a salon kimiyar wancan karnin.
A shekarar 1999 aka kaddamar da shafin blogging mafi suna
wato Blogger.com mallakar kamfanin google.
A shekarar 2003 kuma aka kaddamar da WordPress shafin
Blogging dake kan gaba a yanzu a duniya.
Akwai tarin shafuka da dama da akeyin a yanzu.
[04/02, 10:58 a.m.] Khaleed_Teejohn: *INA FATAN KUN FAHINCI BLOGGING SABO DA HAKA GA YANDA ZAKU KIRKIRI WEBSITE NA BLOG CIKIN SAUKI*👇🏻👇🏻
[04/02, 10:58 a.m.] Khaleed_Teejohn: Abubuwa Bakwai (7) Da Yakamata Ka Sani Kafin
Fara Blogging
.
1. Ka dauki bangaren da zaka maida hankali akai:- a
nan ana son ka dauki bangaren da zaka maida
hakali wajen yin rubutunka misali hikimatv.com.Com ta
mayar da hankali akan harkar internet, computer
da wayar hannu, to kaima ka samu gabar da zaka
maida hankali akanta wadda jama’a zasu sanka
akanta.

2. Ka Fahimci Mabiyanka:- Dolene ka fahimci shin
wane irin mabiya ne da kai? Sannan ka tsara
hanyoyin da zaka dinga amfani dashi wajen isar da
sakonka, misali nace ina kawo labarin wasanni
kuma sai naje nake tallatawa tsofaffi kaga a
yankinmu babu abinda ya shafesu da labarin
wasanni don haka sai nayi amfani da shafukana na
nemi matasa tunda abinda nakeyi sune suke da
bukatarsa.

3. Ka dinga tsara bayanan ka da kuma lokaci kada
kace kullum ka samu content to zaka dinga
sakashi a wannan lokacin, a’a ka dinga tanadin
kaya na yau da na gobe, ta yadda ba zaka sa
mutane su gajiya da kai ba.

4. Ka dinga karanta rubutukan sauran marubuta ka
dinga bibiyar masu yin rubuta mai alaka da abinda
kakeyi.

5. Ka samar da tsayayyen salon rubutunka:- kowa
akwai irin salonsa kamar yadda in kana sauraron
radio sosai to kana jiyo wani shiri zakace wannan
tasha kazace to kaima ka kir-kiri salonka yadda
duk wanda yaga rubutunka zai gane cewa wannan
rubutunka ne.

6. Ka dinga kula sosai da kuskuren rubutu, matukar
baka kiyaye wannan to zaka sanya jama’a su daina
karanta rubutunka.

7. Ka tsara taken rubutu a takaice kuma mai jan
hankali:- Take da shi ne ake jan hankalin jama’a a
rubutu, yana da kyau blogger yayi nazari mai kyau
tare da neman shawara wajen tsara taken
rubutunsa, yana da kyau kafin ka saki rubutu ka
sake duba rubutun.
[04/02, 10:58 a.m.] Khaleed_Teejohn: 4. Menene Banbancin Blog da Websites?
Banbancin website da blog shine shi blog ko yaushe ana so
da an shiga aga sabon kana saka sababbin bayanai akai.
Shi kuma website yawanci an gina shine akan wani bangare
daban wanda in ka ga bayani akai, misali website na
kungiyoyi ana tsara shine yadda idan ka shiga zaka ga
bayanan kungiyar akai duk sanda mutum ya shiga wannan
bayanan zai gani sai dai lokaci bayan lokaci ana iya yin
canje-canje.
A website din ma ana iya saka bangaren blog inda za’a
dinga samun sabbin bayanai shine akan website zaku ga an
saka “blog post”.
5. Waye Blogger?
Wanda ya mallaki blog kuma yake rubuce rubuce akansa shi
ake kira da Blogger.
Idan kana da tambaya ka ajiye min comment

No comments:

Post a Comment